Gameiro zai koma Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gameiro ya ci wa Sevilla kwallaye 29

Atletico Madrid ta sayi dan wasan Sevilla, Kevin Gameiro, a kan kudin da ba a fadi ko nawa ba ne amma rahotanni sun ce kudin sun kai £28m.

Dan wasan, mai shekara 29 ya amince da kwantaragin na shekara hudu.

A na sa ran ranar Asabar din nan kulob din zai duba lafiyar Gameiro.

Kevin Gameiro dai ya zura kwallaye 29 a dukkannin wasannin da ya yi a kakar wasanni da ta gabata.

Sai dai kuma dan wasan bai samu shiga jerin 'yan wasa ba da suka buga gasar kwallon turai ta Euro2016 da aka yi a Faransa.

Gameiro ya je Sevilla daga Paris St-Germain a 2013, a inda ya taimakawa kungiyar ta dauki kofi Europa League har karo uku.

Labarai masu alaka