Hamilton ya lashe gasar tseren motoci ta Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hamilton ya lashe gasar tseren motoci ta Jamus

Lewis Hamilton matukin motar Mercedes ya kankane gasar tseren motoci ta Jamus, har ma ya bai wa abokin tserensa Nico Rosberg tazarar maki 19.

Hamiliton ya jagoranci lashe gasar ne tun lokacin da suka zuba tseren har zuwa karshen, inda Rosberg matukin motar Mercedes ya kammala a mataki na hudu.

An kuma ci tarar Rosberg a gasar, sakamakon kare da ya yi wa Max Verstappen matukin motar Red Bull, wanda dalilin hakan ya sa ya sauka daga kan titin tsere.

Daniel Riccaiardo matukin motar Red Bull shi ne ya yi na biyu a tseren, yayin da Max Verstappen ya kammala gasar a mataki na uku.

An fitar