Olympic: An nada Mikel Obi kyaftin din Nigeria

Image caption A ranar 5 ga watan Agusta za a yi bikin bude gasar Olympic a Brazil

Kociyan tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Nigeria, Samson Siasia, ya nada dan wasan Chelsea, Mikel Obi a matsayin kyaftin din tawagar kasar.

A lokacin da yake sanar da 'yan wasan, Siasia, ya ce nada Obi ya zama wajibi domin shi ne kyaftin din tawagar Super Eagles, kuma shi ne zai jagoranci 'yan wasan da za su wakilci Nigeria a gasar.

A ranar Litinin tawagar matasan 'yan kasa da shekara 23 za ta bar Amurka domin sauka a birnin Rio na Brazil domin fafatawa a fagen tamaula.

Za a fara buga wasannin kwallon kafa kwana biyu kafin a yi bikin bude gasar ta Olympic a ranar 5 ga watan Agusta, wadda Brazil za ta karbi bakunci.

Nigeria wadda ta taba lashe lambar zinare a gasar 1996, tana rukuni na biyu a gasar bana da ya kunshi Sweden da Colombia da kuma Japan.

Labarai masu alaka