Chamberlain zai haskaka a bana — Wenger

Image caption A ranar 13 ga watan Agusta za a fara gasar Premier ta Ingila

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce Alex Oxlade-Chamberlain zai haskaka a kakar wasannin bana, bayan da ya warke daga raunin da ya yi.

Oxlade-Chamberlain, mai shekara 22, ya ci kwallo mai kayatarwa a wasan sada zumunta da Arsenal ta ci Chivas de Guadalajara 3-1 a Amurka.

Sauran 'yan wasan da suka ci wa Arsenal kwallaye sune Chuka Akpom da Rob Holding wanda ya koma Emirates daga Bolton a cikin watan Yuli.

Oxlade-Chamberlain, ya yi rauni ne a gasar cin kofin zakarun Turai da Arsenal ta kara da Barcelona ranar 23 ga watan Fabrairu.

Wenger ya ce kakar bana mai muhimmaci ce ga Oxlade-Chamberlain, kuma "yana kara mana gwiwa da irin salon da yake taka-leda".

Labarai masu alaka