An ci kwallaye 566 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto npfl Twitter
Image caption An kammala wasannin mako na 29 a gasar Firimiyar Nigeria

An ci kwallaye 566 a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka kammala wasanni 258 a ranar Lahadi.

Godwin Obaje na Wikki Tourists ne ke kan gaba a matsayin wanda ya fi cin kwallaye a gasar, inda ya ci 14.

Okiki Afolabi na Sunshine Stars da Abdulrahman Bashir na Nasarawa United suna mataki na biyu, inda kowannensu ya ci 13.

Kano Pillars ce kungiyar da ta fi zura kwallaye a raga, inda ta ci 41, sai Rangers wadda ta ci kwallaye 39 a matsayi na biyu, Akwa United da Wikki Tourist kowaccensu ta ci kwallaye 37 a gasar.

Kungiyar Ikorodu United ce wadda aka fi zura wa kwallaye a raga a gasar, inda aka ci ta 41, sai Akwa United wadda aka ci kwallaye 34 a mataki na biyu.

Labarai masu alaka