"Manyan 'yan wasa ba sa sha'awar Sunderland"

Image caption Moyes ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu a Sunderland

Sabon kociyan Sunderland, David Moyes, ya ce sai kungiyar ta yi namijin kokari a wasanninta, kafin manyan 'yan wasa su yi sha'awar buga mata tamaula.

Moyes na batun ne kan Maroune Fellaini, wanda ya kai Manchester United domin buga kwallo a shekarar 2013.

Fellaini -- wanda ke taka-leda a United -- ya yi aiki karkashin koci David Moyes a kungiyar Everton.

Moyes ya ce kofa a bude take ga duk wani shahararen dan kwallon da yake son komawa Sunderland da murza-leda.

Har yanzu Sunderland ba ta dauki sabon dan wasa ba a bana, sakamakon daukar Sam Allardyce da hukumar kwallon Ingila ta yi domin ya horar da tawagar kwallon kafar kasar.

Sunderland ta dauki Moyes, mai shekara 53, ranar 23 ga watan Yuli kan yarjejeniyar shekara hudu.

Labarai masu alaka