U-17: Nigeria za ta kara da Nijar

Hakkin mallakar hoto Thenff twitter
Image caption Madagascar ce za ta karbi bakuncin gasar matasan Afirka a shekarar 2017

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF, ta ce tawagar matasan kasar 'yan shekara 17 za su kara da ta Nijar a ranar 6 ga watan Agusta a Abuja.

NFF, ta ce kasashen biyu za su kara ne a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin matasa ta Afirka da za a yi a Madagascar a shekarar 2017.

A karawar da kasashen biyu suka yi a bara a gasar matasan Afirka da aka yi a Nijar, Nigeria ce ta samu nasara a kan mai masaukin baki da ci 2-0 a Yamai.

Tuni matasan na Nigeria suka shirya yin wasan sada zumunta da wata makarantar koyon tamaula mai suna tackle Piloter a ranar Laraba.

Sau biyar Nigeria tana lashe kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekara 17.

Labarai masu alaka