Argentina ta dauki koci Edgardo Bauza

Image caption Edgardo Bauza tsohon kociyan Sao Paulo ne

Hukumar kwallon kafa ta Argentina ta nada Edgardo Bauza a matsayin kocin tawagar kwallon kafar kasar.

Bauza, mai shekara 58, tsohon mai horar da Sao Paulo, ya maye gurbin Gerardo Martino wanda ya ajiye aikin bayan da Argentina ta kasa daukar Copa America da aka yi a watan Yuni.

Tun farko an ruwaito cewar Argentina za ta zabi tsakanin kociyan Atletico Madrid, Diego Simeone, da na Tottenham, Mauricio Pochettino a matsayin wanda zai ja ragamar tawagar kwallon kafar kasar.

Bauza zai jagoranci Argentina wasan farko a karawar da za ta yi a cikin watan Satumba a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Sai dai kuma Lionel Messi mai taka-leda a Barcelona, ba zai buga wa Argentina wasan ba, sakamakon yin ritaya daga yi wa kasar tamaula da ya yi bayan Copa America.

Labarai masu alaka