Prince Boateng ya koma Las Palmas

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan kwallon tawagar Ghana, Kevin Prince-Boateng

Dan kwallon tawagar Ghana, Kevin-Prince Boateng, ya koma Las Palmas ta Spaniya kan yarjejeniyar shekara daya.

Boateng, mai shekara 29, ya zauna watanni shida baya buga tamaula, bayan da ya raba gari da Ac Milan.

Las Palmas ce ta bayar da labarain daukar dan kwallon a shafinta na Internet, inda ta ce shi ne fitaccen dan wasa da ya je kungiyar.

A ranar Talata likitocin kungiyar za su duba lafiyar Boateng kafin a gabatar da shi a gaban magoya bayan kungiyar.

Labarai masu alaka