Schalke ta dauki Baba Rahman na Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Baba Rahman tsohon dan wasan Augsburg

Kungiyar Schalke ta Jamus ta dauki dan kwallon Chelsea, Baba Rahman, aro domin ya buga mata tamaula.

Rahman, dan kwallon tawagar Ghana, ya buga wa Augsburg wasanni 51, daga baya ya koma Chelsea a kan yarjejeniyar shekara biyar a watan Agustan bara.

Rahman ya buga wa Chelsea wasan farko a gasar cin kofin zakarun Turai, jumulla ya yi mata wasanni 23.

Dan wasan zai taka-leda a Schalke karkashin kociya Markus Weinzierl wanda ya horar da shi a Augsburg.

Labarai masu alaka