Aston Villa ta sayi McCormack a kan £12m

Hakkin mallakar hoto Getty

Aston Villa ta sayin dan wasan Fulham Ross McCormack a kan £12m.

An yi rade radin cewa dan wasan, dan kasar Scotland yana son komawa Norwich City, sai kawai Villa ta sha gabansu.

McCormack, mai shekara 29, ya koma Fulham daga Leeds United a shekarar 2014 a kan £11m.

Ya zura kwallaye 38 a wasan lig 89 da ya buga wa Fulham, wacce ta kare a matsayi na 20 a gasar cin kofin Zakarun Turai da ta gabata.

Labarai masu alaka