Mohamed Salah ya koma Roma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Salah ya buga wa Fiorentina wasanni 16 a aro daga Chelsea

Dan wasan Chelsea, Mohamed Salah, ya koma kungiyar Roma da taka-leda na din-din-din.

Salah mai shekara 24, dan kwallon tawagar Masar ya buga wa Roma wasanni 34 a kakar bara a matsayin aro daga Chelsea.

Dan kwallon ya koma Chelsea da murza-leda daga Basel kan kudi fan miliyan 11 a watan Janairun 2014.

Bayan da Salah ya buga wa Chelsea wasannin Premier 13 ne ta bayar da shi aro ga Fiorentina a karshen kakar 2014-15.

Labarai masu alaka