Chelsea ta ci Milan a wasan sada zumunta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kante ya lashe kofin Premier da aka kammala a Leicester City

Kungiyar Chelsea ta doke AC Milan da ci 3-1 a wasan sada zumunta don tunkarar wasannin gasar bana a International Champions Cup a Minneapolis.

Bertrand Traore ne ya fara ci wa Chelsea kwallo, daga baya Milan ta farke ta hannun Giacomo Bonaventura.

Dan wasan tawagar Brazil, Oscar, shi ne ya ci wa Chelsea kwallaye biyu a karawar, wadda sabon koci Antonio Conte ya jagoranta.

Sabon dan kwallon da Chelsea ta saya daga Leicester City, N'Golo Kante, ya buga fafatawar kuma wasan farko da ya fara buga wa kungiyar.

Kante wanda ya koma Chelsea kan kudi da ake cewa sun kai fan miliyan Talatin, ya shiga wasan sada zumuntar ne, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Labarai masu alaka