Manchester City na dab da sayen Moreno

Hakkin mallakar hoto Getty

Kungiyar Manchester City na dab da sayen dan wasan kasar Colombia Marlos Moreno.

City za ta sayi dan wasan mai shekara 19 daga wajen kungiyar Atletico Nacional ta kasar Colombia a kan £4.75m, kuma ana sa ran zai fara komawa Deportivo La Coruna a matsayin aro kafin zuwa City.

Moreno ne zai kasance dan wasa na uku da sabon kocin City, Pep Guardiola, ya saya a wannan makon, bayan sayen Leroy Sane daga Schalke da kuma Gabriel Jesus daga Palmeiras.

Guardiola ya kashe fiye da £100m wajen sayen 'yan wasa tun bayan da ya maye gurbin Manuel Pellegrini a matsayin kocin kungiyar a watan Yuli.

Har yanzu dai yana son sayen 'yan wasan tsakiya, inda yake so ya fara da sayen dan wasan Everton, John Stones.

Labarai masu alaka