Babu batun zuwan Sakho West Brom

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption West Brom ba za ta sayar da Saido Berahino ba

Kokarin da West Brom take yi na ganin ta dauki dan kwallon West Ham, Diafra Sakho, ya ci tura bayan da aka gano cewa dan kwallon yana da ciwon baya.

Dan kwallon bai taba fashin shan magani ba, amma ba zai murmure ba kafin a fara Gasar Premier ta bana.

West Brom ta yi shirin daukar Sakho a bana kafin ta sayar da Saido Berahino, dan kwallon da Crystal Palace da Stoke City ke son dauka.

Tuni Stoke City ta taya Saido kan kudi fan miliyan 17, kuma kudin da West Brom ta kayyade za ta sayar da dan kwallon.

Bayan da West Brom ta hakura da sayen Sakho, ita ma ba za ta sayar da Berahino ba.

Labarai masu alaka