An wanke shugaban Fifa daga zargi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Infantino ya zama shugaban Fifa ne bayan korar Blatter

An wanke shugaban Fifa Gianni Infantino daga zargin aikata ba daidai ba bayan wani bincike da aka yi kan yadda yake al'amuransa da daukar ma'aikata da kuma korar masu kwarmata bayanai.

Infantino ya zama shugaban Fifa ne a watan Fabrairu bayan an kori Sepp Blatter.

Kwamitin da'a na Fifa ya ce bai samu shugaban da saba ka'idodjin aiki ba.

Infantino ya ce ya ji dadin wannan hukunci, yana mai cewa "ina godewa dukkan mutanen da suka bayar da hadin kai ga kwamitin da'a domin tabbatarwa gaskiya ta yi halinta".

A watan jiya ne BBC ta fahimci cewa ana gudanar da bincike kan Infantino, mai shekara 46, kan aikata ba daidai ba.

Labarai masu alaka