An kama ɗan damben Morocco da "fyaɗe"

Hakkin mallakar hoto AP

Ƴan sandan Brazil sun kama wani ɗan damben boxing na Morocco bisa zargin yunƙurin yi wa wasu mata masu shara fyaɗe a unguwar wasannin Olympic ta Rio de Janeiro.

An tsare Hassan Saada dan shekara 22 ne a farkon wannan makon, a cewar wata sanarwa ta ƴan sandan.

Ranar Asabar ne dai ɗan damben, wanda zai fafata a ajin masu matsakaicin nauyi, zai yi karawarsa ta farko.

Sai dai wani alƙalin ƙasar Brazil ya bayar da umarnin tsare shi har tsawon kwana 15, lokacin da ake sa ran kammala bincike.

Hakan na nufin ba zai samu damar shiga gasar ba ke nan.

Kafofin yaɗa labarai na Brazil sun ambato ƴan sanda na cewa ɗan damben ya matse ɗaya daga cikin matan a jikin bango, sannan ya yi ƙoƙarin sumbatarta.

Zuwa yanzu dai daga Saada har zuwa jami'an Olympic na Morocco ba wanda ya ce komai.

Labarai masu alaka

Karin bayani