Berlusconi ya sayar da AC Milan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Matsayi na bakwai Milan ta kammala a gasar Serie A da aka yi

Shugaban kungiyar AC Milan, Silvio Berlusconi ya amince ya sayar da kaso sama da 99 da ya mallaki kungiyar ga attajiran China.

An kiyasta AC Milan kan kudi fan miliyan 627 da kuma bashin da yake kanta da ya kai fan miliyan 186.

Attajiran na China masu kamfanin Sino-Europe Sports Investment Management Changxing, sun amince za su kara jarin fan miliyan 297 a Milan din daga nan zuwa shekara uku.

Milan wadda ta lashe kofin zakarun Turai sau bakwai, ta kammala gasar Italiya wadda aka yi a matsayi na bakwai.

Kungiyar ta bi sahun takwararta Inter, wadda wasu attajiran China suka mallaka.

Labarai masu alaka