Man City za ta kara da Steaua Bucharest

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matsayi na hudu City ta yi a gasar Premier da aka kammala

Manchester City za ta fafata da Steaua Bucharest a wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.

Kociyan City, Pep Guardiola ya taba lashe kofin zakarun Turai a Barcelona a shekarar 2009 da 2011.

Celtic kuwa za ta kara ne da Hapoel Beer Sheva, yayin da Dundee za ta kece raini da Legia Warsaw.

Kungiyoyin za su fara wasan farko daga tsakanin 16 da 17 ga watan Agusta, inda za su fafata a wasa na biyu tsakanin 16 da 17 na watan nan.