Dan Kanawa da Bahagon Abba sun buga Canjaras

Image caption Dan Kanawa da Abban Na Bacirawa sun tashi wasan babu kisa

Shagon Dan Kanawa da Bahagon Abban Na Bacirawa sun buga canjaras a damben Lahadi da suka yi a gidan Damben Ali Zuma da ke Dei-Deia a Abuja, Nigeria.

Tun farko Abban Na Bacirawa daga Arewa ne ya bukaci Shagon Dan Kanawa daga Kudu da su taka dambe, shi kuma ya amince suka saka zare, kuma turmi biyu suka yi babu kisa.

Shi kuwa Dogon Minista daga Kudu buge Nokiyar Dogon Sani daga Arewa ya yi a turmin farko, yayin da aka tashi wasa babu kisa tsakanin Audu Dan Kirisfo daga Arewa da Balan Kudawa.

Shi ma damben Autan Faya daga Kudu da Shagon Na Bacirawa daga Arewa babu kisa, haka ma karawar da aka yi tsakanin Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Shagon Fijo daga Arewa babu wanda ya fadi kasa.

Labarai masu alaka