Gernot Rohr zai zama mai horas da Super Eagles

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Gernot Rohr

Kwamitin kwararru na hukumar kwallon kafa ta Najeriya-NFF ya bada shawarar a dauko Gernot Rohr, dan kasar Jamus a matsayin mai horas da 'yan wasan Super Eagles.

Gernot Rohr, mai shekaru 63, kuma tsohon kocin 'yan wasan kwallon kafa na Gabon, da Nijar da kuma Burkina Faso, zai yi aiki da wanda zai taimaka masa, Salisu Yusuf, wanda aka nada a matsayin kocin 'yan wasan a watan jiya.

Nadin da za a yi wa Mista Rohr a wasu kwanaki masu zuwa dai, zai danganta ne da sharuddan kwantiragi da hukumar NFF ta amince da su.

Mataimakin shugaban kwamitin kwararrun na NFF, Ahmed Yusuf Fresh ne ya tabbatar da hakan a shafin intanet na hukumar.

Yusuf Fresh ya ce "kwamitinmu ya gamsu da bayanai kan ko wanene Gernot Rohr, da ayyukan da yake yi yanzu a hukumar kallon kafa ta Jamus, a don haka muka gayyato shi Najeriya don mu tattauna".

"Ya nuna sha'awar aikin sosai, kuma a shirye yake ya zauna a Najeriya. A shirye yake kuma ya yi aiki da masu horas da 'yan wasa na cikin gida, sannan yayi amanna kungiyar Super Eagles za ta iya samun shiga gasar kwallon kafa ta duniya a 2018, abin da ke da muhimmanci ga NFF", inji Yusuf Fresh.

Sunday Oliseh ne mai horas da 'yan wasan na Super Eagles kafin ya ajiye aikin a watan Fabrairu saboda takaddama kan kwantiraginsa.

Labarai masu alaka