Man U na gab da kammala cinikin Pogba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paul Pogba

Kulob din Manchester United ya na gab da kammala yarjejeniyar sayo dan wasan Juventus Paul Pogba a kan kudi fam miliyan dari.

Za a duba lafiyar dan wasan mai shekaru 23 a 'yan kwanaki masu zuwa kafin a kammala cinikinsa, wanda zai zama mafi tsada a tarihin sayen 'yan wasan kwallon kafa a duniya.

Pogba wanda ya bar kulob din Manchester a kan kudi fam miliyan daya da rabi a 2012, yanzu zai koma kulob din a kan kudin da ya haura fam miliyan tamanin da biyar da Real Madrid ta sayi Gareth Bale a 2013.

Har yanzu ba a gama daidaitawa ba a kan sharuddan da suka shafi dan wasan dake bugawa Faransa tsakiya, koda yake a na ganin hakan ba wani abin jidali ba ne.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce yana so a kammala cinikin dan wasan ne bayan kulob din ya yi wasansa na farko a gasar Premier a Bournemouth ranar 14 ga watan Agusta.

Labarai masu alaka