Nigeria ta kai wasan daf da na kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Nigeria za ta kara da Colombia a wasa na karshe a cikin rukuni na biyu

Tawagar Nigeria ta matasa 'yan kasa da shekara 23 ta doke ta Sweden da ci daya mai ban haushi a wasan kwallon kafa a gasar Olympic da ake yi a birnin Rio na Brazil.

Nigeria ta ci kwallon ne ta hannun Sadiq Umar ana saura minti biyar a tafi hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon, Nigeria ta kai wasan daf da na kusa da karshe, bayan da ta samu nasara a wasanni biyu da ta buga a gasar.

Za ta buga wasan gaba kuma na karshe a cikin rukuni na biyu da Colombia a ranar Laraba 10 ga watan Agusta.

Labarai masu alaka