'Yan wasan Firimiyar Nigeria sun nufi Spaniya

Hakkin mallakar hoto Twitter NPFL
Image caption 'Yan wasan Firimiya za su fara fafatawa da Malaga

Da safiyar Litinin ake sa ran 'yan wasan da suke buga gasar Firimiyar Nigeria, za su sauka a Spaniya domin buga wasanni da wasu kungiyoyin gasar La Liga.

Kociyan tawagar Nigeria, Salisu Yusuf ya tafi da 'yan wasa 25, wadanda za su kara a gasar Carranza Wold Cup da za a fara a ranar Laraba 12 ga watan Agusta a birnin Cadiz da ke Spaniya.

A kuma ranar ne 'yan wasan na Firimiyar Nigeria za su yi wasan farko da Malaga, idan sun samu nasara su kai wasan karshe a gasar.

Idan suka yi rashin nasara sai su fafata a neman mataki na uku tsakanin wadda aka doke a fafatawar da za a yi da Atletico Madrid ko kuma Cadiz CF.

Karawar da kungiyoyin za su yi, ta biyo bayan kulla yarjejeniya da gasar Firimiyar Nigeria ta kulla da ta La Liga domin aiki tare.

Labarai masu alaka