An fitar da Djokovic daga gasar Olympic

Hakkin mallakar hoto Reuters

Juan Martin Del Potro ya fitar da Novak Djokovic wanda yake matsayi na daya a iya kwallon tennis a duniya daga gasar Olympic ta Brazil.

Del Potro ya samu nasara ne a kan Djokovic da ci 7-6 (7-4) 7-6 (7-2).

Djokovic ya fice daga filin wasa yana kuka, bayan da suka kammala karawar da suka yi awa biyu da rabi.

Dan kasar Serbia wanda bai taba lashe lambar yabo a wasannin Olympic ya ce wannan ne wasan da ya buga mafi muni a tarihi.

Labarai masu alaka