An hana Rasha shiga Olympic na nakasassu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Birnin Rio ne zai karbi bakuncin wasan nakasassu da ake kira Paralympic na bana

Kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya soke Rasha daga shiga wasannin bana, sakamakon zargin da ake yi wa 'yan wasan kasar da amfani da abubuwa masu kara kuzari.

Kwamitin ya yanke wannan hukuncin ne, bayan ya yi nazarin da rahoton da McLaren ya fitar a makon jiya, wanda ya fayyace yadda Rasha ta dauki nauyin wani shiri kan amfani da abubuwa masu kara kuzarin wasanni.

Kwamitin Olympic na nakasassun Rasha zai iya daukaka kara kan wannan hukunci a kotun daukaka karar wasanni ta duniya.

Za a fara wasannin Olympic na nakasassu a birnin Rio daga ranar 7 ga watan Satumba, kuma 'yan wasa Rasha 267 ba za su sami damar shiga wasannin ba.

Labarai masu alaka