Brazil da Iraq sun buga canjaras a tamaula

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Brazil tana mataki na uku a rukunin farko da maki biyu

Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Brazil da ta Iraq sun tashi canjaras babu ci a wasan kwallon kafa da suka buga a gasr Olympic.

Brazil wadda ke karbar bakuncin wasannin bana, wadda Neymar mai taka leda a Barcelona ke jagoranta ta kasa zura kwallo a ragar abokiyar karawarta.

Wannan ne karo na biyu da Brazil ta kasa zura kwallo a raga, bayan da ta fara yin canjaras da Afirka ta Kudu.

Brazil wadda ta lashe kofin duniya sau biyar a fagen tamaula ta kasa lashe lambar zinare a fagen tamaula a wasannin Olympics.

Labarai masu alaka