Ko sutura na da tasiri a cin wasa?

Image caption Germany ta ci Egypt 2-0

'Yan wasan kwallon hannu na mata na kasar Misra sun sanya kayan da suka rufe jikinsu amma kuma sai ga shi 'yan wasan Jamus da suka sanya rigar mama da kamfai sun ci su 2-0.

Kungiyoyin biyu dai sun fafata ne a wasannin gasar Olympics, ranar Litinin.

Su dai 'yan wasan Misran sun sanya kayan da suka rufe duka jikinsu da karamin hijabi, a inda su kuma 'yan Jamus suka sanya rigar mama da kamfai irin na masu shiga ruwa.

To mai hakan yake nunawa?

Wasu na ganin cewa kayan da 'yan wasan na Misra suka sanya ba za su ba su damar sakewa su yi wasa ba, al'amarin da ya sa takwarorin nasu na Jamus suka lallasa su.

To amma wasu na da ra'ayin cewa banbancin suturar dai ya nuna irin yadda kasashen biyu suka sha ban-ban dangane da al'ada da addini.

Sai dai kuma hakan na nufin irirn wadannan wasanni za su iya taka rawa wajen fahimtar al'ada da addinin juna domin wanzuwar zaman lafiya, a duniya.

Labarai masu alaka