Everton ta sayi Yannick Bolasie

Hakkin mallakar hoto AFP

Kulob din Everton ya sayi dan wasan gaba na DR Congo Yannick Bolasie kan kudi fan miliyan 25 daga Crystal Palace.

Dan wasan mai shekaru 27, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

Ya shafe kakar wasanni hudu a Palace tun bayan da ya koma kungiyar daga kulob din Bristol a 2012.

Ya murza-leda sau 143 a Palace, inda ya zura kwallaye 13.

An sako shi a zageye na biyu a wasan da Palace ta sha kayi a hannun West Brom da ci 1-0 a ranar Asabar.

Bolasie ya ce ba kudi ne suka sanya shi ya koma Everton ba, illa dai kawai yana son cigaba ne a rayuwarsa ta kwallo.

Labarai masu alaka