Gareth Bale ba zai buga Super Cup ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ce ta dauki kofin zakarun Turai, Sevilla kuwa ta ci na Europa

Dan wasan tawagar Wales, Gareth Bale, ba zai buga wa Real Madrid wasan Super Cup da za ta yi da Sevilla a ranar Talata ba.

Bale mai shekara 27, da Toni Kross na Jamus ba sa cikin 'yan wasan da za su buga wa Madrid sakamakon dogon hutun da suka yi, bayan kammala gasar kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa.

Pepe da Cristiano Ronaldo 'yan kwallon tawagar Portugal, wadan da suka lashe kofin nahiyar Turai na bana, su ma ba za su buga karawar ba.

Real Madrid ce ta lashe kofin zakarun Turai da aka kammala, yayin da Sevilla ce ta dauki na Europa, kuma kungiyoyin biyu za su kara ne a Trondheim.

Labarai masu alaka