Musulma Ba’amurkiya ta farko a gasar Olympic

Hakkin mallakar hoto AP

Ibtihaj Muhammad ta kafa tarihi ta hanyar zama Ba’amurkiya Musulma ta farko da ta taba shiga gasar Olympic, inda za a fafata da ita a wasan takobi.

Gab da fara gasar ne dai hankalin kafafen watsa labarai ya karkata a kan Ibtihaj, wadda saboda kwazonta mujallar Time ta sanya ta cikin mata 100 da suka fi tasiri a duniya, kuma kamfanin katin lamuni na Visa ya sanya ta a sahun gaba a cikin wadanda suke masa talla.

Ta samu daukaka a fannin wasanni domin a shekarar 2007 zuwa 2008 tana cikin ‘yan wasa 113 da ke sahun gaba a duniya, amma a wannan kakar wasannin ta komo matsayi na takwas.

Kuma ta samu lambar yabo ta nahiyar Amurka a watan Yunin 2016, bayan matar da ta ci zinare sau biyu a jere, Mariel Zagunis, ta janye saboda raunin da ta yi.

A shekarar 2014 ne kuma Ibtihaj ta ci zinare wa tawagar Amurka a wasan takobi na duniya da aka yi a Rasha.

‘Ban taba tunanin zan yi wasa a gasar Olympic ba, ' In ji Ibtihaj, wadda iyayenta suka zo daga kudancin Amurka domin kallon wasan da za ta yi. ‘Sai dai kuma lokaci ne mai matukar muhimmanci a rayuwa ta ina dokin wakiltar ba kaina ko iyalina ko kasa ta kawai ba har ma daukacin al’ummar Musulmi.’

Hakkin mallakar hoto Getty

Zabenta a cikin tawagar Amurka ta 'yan wasan takobi ya zo ne a daidai lokacin da wasu za su ce ake samun karuwar mata a fagen siyasar duniya da kuma a fagen wasanni.

Kuma a matsayinta na ‘yar wasan motsa jiki, sanya hijabi kamar yadda addininta na Musulunci ya tanada ya sa ta fita daban.

Hasali ma dai ta fara wasan takobi ne tana da shekaru 12 a duniya, saboda shi kadai ne wasan da za ta sanya suturar da ke rufe dukkannin sassan jikinta.

Mace ce wadda ba ta boye imaninta da kuma muhimmancin sanya hijabi a wurinta duk da cewa a kasar da ta fito Musulmi kashi daya cikin dari ne kacal na mutane miliyan 324 da ke Amurka.

Sai dai ta kan fuskanci kalubale, kamar a wajen wani wasan takobi da aka yi a jihar Texas, inda aka bukaci ta cire dankwalinta.

Yayin da a watan Afrilu ne kuma lokacin da take tafiya a kan titi wani mutum saboda yana yi mata kallon wata mara gaskiya, ya yi tunanin ko za ta tayar da bam ne.

Sai dai hakan wani bangare ne na sunan da ta yi.

A lokacin bikin salla bayan kammala azumin watan Ramadan, an gayyace ta fadar White House, inda shugaban Amurka, Barak Obama, ya zolaye ta da cewa ‘Ba wanda zai matsa mata saboda za ta yi wasa da hijabi a Olympics.

Ibtihaj kuma ta koya wa uwargidar Obama, Michelle, wasan takobi a New York, a wani bangare na kwana 100 kafin fara wasan Olympics.

Hakkin mallakar hoto facebook

Labarai masu alaka