Inter Milan ta raba gari da Mancini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Frank de Boer tsohon dan wasan Ajax da Barcelona

Inter Milan ta nada Frank de Boer a matsayin sabon kociyanta, bayan da ta raba gari da Roberto Mancini.

Manciniya bar aikin ne bisa wani rahoto da ke cewar shi da mahukuntan kungiyar sun kasa cimma matsaya kan saye da sayar da 'yan wasan Inter din.

Wannan ne karo na biyu da Mancini ya jagoranci Inter wadda ta kare a mataki na hudu a kan teburin Serie A da aka kammala a bana.

Wasu attajiran China ne suka sayi Inter a watan Yuni, kuma a ranar Juma'a Tottenham ta ci Inter 6-1 a wasan sada zumunta a ranar Juma'a.