Paul Pogba ya isa Manchester United

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Pogba ya bar United a shekarar 2012 ya koma Italiya da taka-leda

Paul Pogba ya isa Manchester United domin a duba lafiyarsa kan batun komawa can da taka-leda kan kudi fan miliyan 89 daga Juventus.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Faransa, ya sauka a filin jirgin sama na Manchester daga Nice, daga nan ne ya wuce filin atisaye na United.

United za ta biya Juventus Yuro miliyan 105 kudin sayen Pogba da karin kudin ladan wasanni da sauran hidimomi.

Idan United ta sayi Pogba daga Juventus, zai zama dan kwallon kafa da ya fi tsada a duniya, bayan Gareth Bale da Real Madrid ta saya kan kudi fan miliyan 85 a shekarar 2013 daga Tottenham.

Pogba ya bar United kan kudi fan miliyan daya da dubu dari biyar a shekarar 2012.

Labarai masu alaka