Manchester United ta sayi Paul Pogba

Hakkin mallakar hoto Getty

Manchester United ta sayi Paul Pogba kan kudi fan miliyan 89 kan yarjejeniyar shekara biyar daga Juventus.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Faransa, ya koma United ne shekara hudu bayan ya bar Old Trafford zuwa Juventus kan fan miliyan daya da rabi a shekarar 2012.

Pogba ya ce United ce kungiyar da ta dace da shi, wadda yake sa ran zai cimma burinsa a fagen tamaula a duniya.

Pogba ya zama dan kwallon kafa da aka saya mafi tsada a duniya, bayan Gareth Bale da Real Madrid ta saya kan kudi fan miliyan 85 a shekarar 2013 daga Tottenham.

Kocin kungiyar Jose Mourinho ya ce Pogba ne zai zama "ruhin Manchester United" nan da shekara goma da ke tafe.

Labarai masu alaka