West Ham ta sayi Masuaku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arthur Masuaku lokacin da yake Olympiakos

Dan wasan baya na Olympiakos, Arthur Masuaku zai koma West Ham a kan kwantaragin shekara hudu.

Dan wasan mai shekara 22, ya fara buga kwallo a kulob din Valenciennes, kifin daga bisani ya koma Olympiakos a 2014.

Masuaku ya dauki kofi daban-daban a jere ga kungiyar ta Girka da suka hada da wasannin da ya buga 12 a gasar Zakarun Turai.

Tauraruwar dan wasan ta fara haskawa tare da ta Paul Pogba, a lokacin suna bugawa Faransa wasa na 'yan kasa da shekara 18, a 2011.

Labarai masu alaka