An tsare dan damben Namibiya kan fyade

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan dambe na biyu da aka kama daga Afirka kan zargin fyade a birnin Rio

'Yan sanda a Brazil sun kama wani dan damben boksin na Namibiya, Jonas Junius, kan zargin yunkurin aikata fyade a wurin kwanan 'yan wasan gasar Olympic.

Junius, mai wasan ajin matsakaita nauyi wanda ya kamata ya dambata da Hassan Amzile a ranar Alhamis, yana tsare bisa yunkurin rungume wata mai aikace-aikace a sansanin tare da sunbatar ta.

An kama Junius a ranar Litinin, wanda shi ne ya jagoranci da ga tutar Namibia a ranar bikin buge gasar Olympic a birnin Rio, yana can a tsare ana yi masa tambayoyi.

Ko a ranar Juma'a sai da 'yan sandan Brazil suka kama wani dan damben boxing na Morocco bisa zargin yunkurin yi wa wasu mata masu shara fyade..

Labarai masu alaka