Nigeria ta kai zagayen gaba a tennis din teburi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Quadri ya zama dan Afirka na farko da ya kai wasan daf da na kusa da karshe a kwallon tebur a Olympic

Dan wasan Nigeria, Aruna Quadri, ya zama dan Afirka na farko da ya kai wasan daf da na kusa da karshe a wasan kwallon tennis na tebur.

Quadrin ya kai wannan matakin ne bayan da ya doke dan wasan Jamus, Timo Boll da ci 4-2 a karawar wasannin zagaye na hudu da suka yi.

Dan wasan na Nigeria, ya samu nasarar doke Boll wanda shi ne ke mataki na 13 a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis na tebur a duniya a minti 16.

Wannan kuma shi ne karo na biyu da Quadri ke wakiltar Nigeria a wasannin Olympic.

Labarai masu alaka