PSG ta dauki Jese na Real Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jese ya lashe kofin zakarun Turai guda biyu a Real Madrid

Paris St-Germain ta dauki dan wasan tawagar Spaniya, Jese, daga Real Madrid kan yarjejeniyar shekara biyar.

Jese mai shekara 23, ya koma Real Madrid yana da shekara 14, kuma yana daga cikin 'yan wasan Madrid da suka dauki kofin zakarun Turai a shekarar 2014 da kuma 2016.

Dan kwallon zai yi aiki karkashin tsohon kociyan Sevilla, Unai Emery, wanda ya maye gurbin Lauren Blanc a PSG a watan Yuni.

Jese ya ce abin alfahari ne da zai buga tamaula karkashin Unai Emery, wanda ya kware a fagen horar da tamaula.

Labarai masu alaka