Ayew ya koma West Ham da taka-leda

Hakkin mallakar hoto Premier League
Image caption Ayew ya koma kungiyar Swansea City a shekarar 2015

Dan wasan tawagar Ghana, Andre Ayew, ya koma West Ham da murza-leda kan kudi fan miliyan 20 da dubu dari biyar daga Swansea City.

Ayew mai shekara 26, ya koma Swansea a watan Yunin 2015, bayan da yarjejeniyarsa ta kare da Marseille, ya kuma ci kwallaye 12 a gasar Premier da aka kammala.

Ayew ne dan kwallo na biyar da West Ham ta saya a bana, bayan Sofiane Feghouli da Havard Nordtveit da Ashley Fletcher da kuma Arthur Masuaku.

A ranar 13 ga watan Agusta ne za a fara wasannin gasar Premier shekarar nan.

Labarai masu alaka