Arsenal: Gabriel ya samu rauni

Image caption Gabriel a wani wasa da Watford

Dan wasan baya na Arsenal, Gabriel Paulista ba zai taka leda ba har tsawon mako shida zuwa takwas sakamakon raunin da ya samu a agararsa.

Ranar Lahadi ne dai Arsenal ta taka leda da Liverpool, a wasannnin share fagen gasar Premier ta Ingila.

Raunin da dan wasan ya samu, ya ba wa dan wasan Valencia, Shkodran Mustafi damar zuwa kungiyar wasan.

An dai ce Arsenal na zawarcin Mustafi mai shekara 24, a kan kudi £30m.

Daman Per Mertesacker ya yi wata biyar ba ya taka leda sakamakon raunin da ya samu a gwiwarsa.

Shi ma Laurent Koscielny ya dawo yin atasaye ranar Litinin.

Labarai masu alaka