Ashley Williams zai koma Everton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ashley ne kyaftin din Wales a gasar Euro2016

Kulob din Swansea City ya amince da ya saki kyaftin din kungiyar, Ashley Williams zuwa Everton, a kan kudi £12m.

Ashley ya kwashe shekaru takwas a kungiyar ta Swansea.

Tun da farko dai sai da Swansea ta yi watsi da tayin da Everton din ta yi mata dangane da dan wasan a kan £10m, a farkon wannan wata.

Williams, wanda kwantaraginsa a Swansea ya kamata ya kai har 2018, ya buga wasanni fiye da 300, tun bayan da ya je kulob din a watan Maris na 2008.

Asheley Williams ya je Swansea ne daga Stockport.

Labarai masu alaka