An naɗa Gernot Rohr kocin Super Eagles

Image caption Gernot Rohr, sabon kocin Super Eagles.

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF ta nada Gernot Rohr a matsayin mai horas da kungiyar wasan kasar, Super Eagles.

Hukumar ta NFF da Gernot Rohr sun amince da horas da kungiyar na tsawon shekara biyu.

An dai kafa wa mista Gernot sharadin kai kungiyar ta Super Eagles ga wasan karshe na gasar kwallon kafa ta duniya ta 2018, da za a yi a Russia.

A watan da ya gabata ne dai hukumar ta NFF ta nada dan kasar Faransa, Paul Le Guen a matsayin kocin kungiyar amma Le Guen din ya yi watsi da nadin.

Wane ne Gernot Rohr?

Gernot Rohr, mai shekara 63, Bajamushe ne wanda kuma ya kasance tsohon dan wasan baya na kasar tasa Jamus.

Ya kuma horas da 'yan wasan kulob din Bordeaux na Faransa da Etoile du Sahel na kasar Tunisia.

Mista Rohr ya horas da 'yan wasan kungiyoyin kwallon kafar Gabon da Niger da Burkina Faso.

Kalubalen da ke gaban Rohr

Gernot Rohr zai yi fitar farko da 'yan wasan Super Eagles zuwa birnin Fatakwal da ke kudancin Najeriyar, a inda kungiyar za ta karbi bakuncin 'yan wasan kasar Tanzania.

Kungiyoyin biyu dai za su kara ne a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2017 wato Africa Cup of Nations.

Duk da cewa dukannin kasashen ba za su shiga gasar ba, amma wasan zai zama gwaji ga sabon kocin na Super Eagles, Gernot Rohr.

Wasan ne zai zama 'yar manuniya ga irin rawar da sabon kocin zai taka a wasan da Najeriya za ta buga da Zambia ranar 3 ga watan Octoba.

Najeriyar dai za ta fafata da Zambia ne domin neman gurbin cancantar shiga gasar kwallon kafa ta duniya da za a yi a 2018 a Russia.

Har wa yau, Najeriyar za ta kara da Cameroon da Algeria duka a wasannin neman gurbin shiga gasar ta kwallon duniya.

Labarai masu alaka