Real Madrid ta lashe UEFA Super Cup

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Kofi na biyu da Zidane ya lashe a matsayinsa na kociyan Madrid

Kungiyar Real Madrid ta lashe UEFA Super cup, bayan da ta ci Sevilla 3-2 a karawar da suka yi a ranar Talata.

Real Madrid ce ta fara cin kwallo ta hannun Marco Asensio a minti na 21 da fara wasa, kuma daf da za a je hutu ne Sevilla ta farke ta hannun Franco Vazquez.

Saura minti 12 a tashi daga wasan ne Sevilla ta kara cin ta biyu ta hannun Yevhen Konoplyanka, sai dai kuma Madrid ta farke ta hannun Sergio Ramos.

Bayan da aka yi karin lokaci ne Real Madrid ta ci kwallo na uku ta hannun Daniel Carvajal, wanda hakan ya sa ta lashe kofin bana.

Da kuma wannan sakamakon Real Madrid ta dauki UEFA Super cup na uku kenan, yayin da Sevilla ke da shi guda daya.

Ana buga kofin ne tsakanin wadda ta lashe kofin zakarun Turai da aka kammala da kuma wadda ta ci na Europa a shekarar.

Labarai masu alaka