Stones ne dan wasa na biyu mafi tsada

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption John Stones ne dan wasa na biyu mafi tsada

Manchester City ta sayi dan wasan Everton, John Stones a kan £47.5m.

Wannan ya sanya Stones zama dan wasan baya na biyu mafi tsada da aka saya a wannan shekarar.

Dan wasan dai ya rattaba hannu ne a kan kwantaragin zama a kulob din na tsawon shekara shida.

Kuma shi ne dan wasa na takwas da kociyan Man City, Pep Guardiola ya kawo kulob din tun zuwansa.

A wata sanarwa,kungiyar Everton ta sanar da karbar makudan kudi domin sakin Stones din zuwa Manchester City.

John Stones dai ya koma Everton ne a 2013 daga Bernsley a kan £3m.

Labarai masu alaka