Ba tabbas zamana a Arsenal — Wenger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsene Wenger ya je Arsenal a 1996

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce cigaba da zamansa a kulob din zai ta'allaka ne ga rawar da kungiyar za ta taka a kakar wasannin Premier ta bana.

Arsene, mai shekara 66 ya fara horas da 'yan wasan Arsenal ne a watan Satumbar 1996 kuma a watan Yunin shekara mai zuwa ne kwantaraginsa zai kare.

Tun dai 2004, kulob din na Arsenal bai kara daukar kofin Premier ba, al'amarin da ya sa Wenger yake fuskantar matsin lamba da magoya bayan kulob din.

Wenger ya shaidawa BBC cewa " Kwantaragina zai kare a shekara mai kamawa. Zan zabi cigaba da zama ko barin kulob din bayan na ga irin rawar da kungiyar za ta taka a wasannin wannan kakar."

A baya dai an yi ta tunanin Arsene Wenger na zawarcin zama kocin kasar Ingila domin maye gurbin Roy Hodgson, kafin a nada Sam Allardyce a matsayin mai horas da kungiyar.

A ranar Lahadi ne dai Arsenal za ta fafata da Liverpool a wasannin share fagen shiga gasar Premier League.

Labarai masu alaka