Brazil ta kai zagayen gaba a tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brazil za ta kara da Colombia a wasan zagayen gaba

Tawagar Brazil ta matasa 'yan kasa da shekara 23 ta kai wasan daf da na kusa da karshe, bayan da ta ci Denmark 4-0 a wasan kwallon kafa.

Brazil mai masaukin baki ta ci kwallaye biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci ta hannun Gabriel Barbosa da kuma Gabriel Jesus.

Bayan da aka dawo daga hutu ne ta kara zura kwallaye biyu a ragar Denmark ta hannun Wallace Oliveira dos Santos da kuma Gabriel Barbosa.

Brazil wadda ba ta taba lashe lambar zinariya ba a wasan kwallon kafa a Olympic, ta jagoranci rukunin farko da maki biyar, sai Denmark ta biyu da maki hudu.

Fafatawa tsakanin Iraqi da Afirka ta Kudu tashi suka yi kunnen doki.

Labarai masu alaka