Liverpool za ta kara da Burton Albion

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun daga ranar 22 ga watan Agusta za a fara buga wasannin zagaye na biyu a Capital One Cup

Liverpool za ta ziyarci Burton Albion a Capital One Cup na bana wasannin zagaye na biyu.

Chelsea kuwa za ta kara ne tsakanin Bristol Rovers ko Bristol City, yayin da Everton za ta kece raini da Yeovil mai buga League Two a Ingila.

Kimanin kungiyoyi 13 ne za su yi gumurzu a karawar zagaye na biyu a Capital One Cup wasannin zagaye na biyu.

Za a fara karon batta a kofin da Manchester City ta dauka a gasar da aka kammala a ranar 22 ga watan Agusta,

Labarai masu alaka