Tawagar Colombia ta ci ta Nigeria 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ce ta jagoranci rukuni na biyu, yayin da Colombia ta yi na biyu

Tawagar kwallon kafa ta Colombia ta doke ta Nigeria da ci 2-0 a wasan kwallon kafar maza da suka kara a wasan Olympic a birnin Rio.

Colombia ta fara cin kwallo a minti na hudu da fara wasa ta hannun Teofilo Gutierrez, bayan da aka dawo daga hutu ne ta kara ta biyu a bugun fenariti ta hannun Dorlan Pabon.

Duk da rashin nasarar da Nigeria ta yi a hannun Colombia, ita ce ta jagoranci rukuni na biyu da maki shida, ta kuma kai wasan daf da na kusa da karshe.

Colombia ce ta yi ta biyu a rukunin da maki biyar, yayin da Japan ta kammala a mataki na uku da maki hudu, sai Sweden ta karshe da maki daya kacal.

Nigeria za ta buga wasan zagayen gaba da tawagar da ta yi ta biyu a rukunin farko a ranar Asabar 13 ga watan Agusta.

Labarai masu alaka