Man United da City sun fi kashe kudi a tsaro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyoyin birnin Manchester ne ke kan gaba wajen kashe kudi kan tsaro a wasannin kwallon kafa a Ingila

Kungiyar Manchester City da Manchester United sun fi kowacce kungiyar da ke Ingila yawan kashe kudi a wajen tsaro a lokacin tamaula.

Manchester City ce ke kan gaba inda ta bai wa Great Manchester Police ladan kudin tsaro fan 944,192 sai United da ta kashe fan 925,126 a kakar da ta wuce.

An caji Arsenal da Chelsea da Crystal Palace da Tottenham da kuma West Ham fan 178,047 jumulla kan ladan tsaro a lokacin wasanninsu.

Jami'an tsaron sun se suna cajar kungiyoyin ne kan yawan 'yan sansa da suka buka ci a tura aiki a lokacin wasan tamaula.

'Yan sanda kan yi fama da kalubale a lokacin da ake buga wasannin Premier musamman a wasannin hamayya.

Labarai masu alaka