Olympic: Phelps ya ci zinare na 22 a linkaya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya lashe lambobin zinare 21 a tarihin Olympic

Dan kasar Amurka, Michael Phelps, ya lashe lambar zinare na 21 jumulla a gasar Olympic a wasan linkaya.

Dan wasan ya ci zinare na 20 ne, bayan da ya doke Chad le Clos zakaran gasar 2012 a tseren mita 200.

Phelps dan Amurka mai shekara 31, ya samu nasara a cikin minti daya da dakika 53, yayin da dan wasan Afirka ta Kudu Chad le Clos ya kammala a mataki na hudu.

Phelps ya dauki fansar doke shi da Le Clos mai shekara 29 ya yi a gasar Olympic da birnin Landan ya karbi bakunci a shekarar 2012.

Labarai masu alaka